Ta'addanci: Bam Ya Hallaka Wani Dansanda a Masar

  • Ibrahim Garba

Shugaba Abdel-Fattah el-Sisi na Masar

Yayin da Kubdawan kasar Masar ke harmar harkokin ibadarsu daga gobe Litini, wani bam ya tashi yayin da ake kokarin kwance shi daura da wata majami'ar Kubdawan ya hallaka wani dan sanda, baya ga wadanda ya raunata.

Jami'ai a Masar sun ce wani dansanda ya mutu yayin da ya ke kokarin kwance wani bam, wanda aka dana daura da wata majami'a da ke bayan garin Alkhahira, babban birnin kasar.

Hukumomi sun ce wasu 'yansandan kuma a kalla biyu sun samu raunuka a wannan fashewa ta jiya Asabar.

Kafar labarai ta Reuters ta ce an bankado bam din ne cikin wata jakar da aka ajiye a kan rufin gini.

Wannan na faruwa a daidai lokacin da Kubdawa Kirista na Masar ke shirin Kirsimetinsu a gobe Litini.

Nan take dai babu wanda ya dau alhakin wannan al'amarin.

To sai dai kungiyar ISIS ta sha ikirarin kai hare-hare kan Kiristan kasar ta Masar.