Syria ta zafafa matakan soji da take dauka kan masu zanga-zangar rajin Demokuradiyya,yayinda kasar take kara fuskantar matsin lambar kasa da kasa kan wadan nan matakan da take dauka.
An bada rahoton harbe-harbe a garin Daraa na kasar Sham (Syria) inda sojan gwamnati ke ci gaba da kokarin murkushe zanga-zangar masu neman kawo chanji a harakokin mulki na kasar.
Ba wata alama dake nuna cewa an kusa jingine matakin murkushe masu zanga-zagar da gwamanti ke dauka, wanda ya hada anfani da tankunan yaki da tarin sojoji. Rahottani sunce yanzu mutanen garin Daraa na cikin fargaba sosai, har basa iya barin gidajensu, su fita waje.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sunce sojojin Syria suna tsare da mutane da suka kamo daga sassan kasar daban-daban. Shedu da ‘yan hankoron kare hakkin bil adama sunce a jiya kadai an kashe mutane sun kai 20 a lokacinda sojan gwamanati suka shiga garin na Daraa.