Tunda farko a jiya Alhamis, sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, yace "yana da tsammanin" zata yi wuya a cimma tsagaita wuta da kasar Rasha na kawo karshen fada a Aleppo.
Bayan da suka gana da Lavrov a binrin Hamburg jiya Alhamis, Kerry ya gayawa manema labarai cewa yana dakon "wasu bayanai da shawarwari"," ya kara da cewa "muna aiki kan wani abu a nan" ba tareda ya bada karin bayani ba.
A binrin New York, jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin na Syria, Staffan de Mistura, yayi marhabin lale da sanarwar da Rasha ta bayar, duk da haka ya gayawa manema labarai cewa bashi da masaniyar ko an daina yaki, kuma ko an kwashe farar hula ba.
Majalisar Dinkin Duniya zata halarci taron da za'a yi gobe Asabar tsakanin manyan kasashen dangane da wannan rikici. Za'a yi ganawar ce a birnin Geneva.