Sweden Ta Dauki Wasu Matakai Na Daban Wajen Yakar COVID-19

Yayin da mafi kasarin yankin nahiyar Turai ke karkashin tsauraran dokar hana fita sanadiyyar cutar coronavirus, kasar Sweden ta dauki wasu matakai da suka sa ta sha banban da sauran kasashen nahiyar.

Su dai hukumomin kasar sun ki daukar matakan rufe harkokin yau da kullum inda aka bar jama’ar kasar suna fita aiki tare da yin tafiye-tafiye.

Tun farkon barkewar cutar ta COVID-19, hukumomin kasar Sweden suka dauki matakan da suka dace yayin da cutar take salwantar da rayuka a Italiya, Spain, Faransa da kuma Burtaniya, ko da yake kasar ta ga karuwar adadin mace-mace da suka doshi dubu hudu, lamarin da ya jefa al’umar kasar cikin yanayi na fargaba.

Sai dai ba kamar sauran biranen kasashen nahiyar Turai ba, Stockholm, babban birnin Sweden ya ci gaba da ganin hada-hadar jama’a inda shaguna, da gidajen rawa suka ci gaba da kasancewa a bude tare da makarantun firamare da wuraren gyaran gashi.

Matakin da suka dauka dai shi ne, gwamnati ta umurci kowanne mutum, ya dauki alhakin kula da kansa ta hanyar yin nesa-nesa da juna.

Sannan an umurci mutane da shekarunsu suka haura 70 da marasa lafiya su zauna a gida.

Masana a harkar kiwon lafiya sun ce wannan nasara da kasar ta Sweden ta samu wajen dakile yawan mace-mace na da alaka da yadda suka dore wajen bin ka’idojin kare yaduwar cutar.