WASHINGTON, DC —
‘Yan kungiyar kwallon kafar Najeriya, ta mata watau Super Falcons, sun lashe kofin kwallon kafa na mata na nahiyar Afirka, a wasan karshe da aka buga a kasar Kamar, bayan da suka doke kasar ta Kamaru da ci daya mai banhaushi.
‘Yan Super Falcons, din sun jefa kwallon ne bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, inda Desire Oparanozie, ta sami nasarar jefa kwallon a ragar Kamaru.
‘Yan Super Falcons a yanzu haka sun sauka a Najeriya, kuma ana sa ran cewa shugaba Muhammadu Buhari, zai karbi bakuncinsu a fadar Gwamnati dake Aso Villa.
Wannan shine karo na takwas, ‘yan kungiyar Super Falcons, ke lashe wannan kofin sun lashe a shekarun 1998, 2000, 2002, 2004,2006, 2010, 2014 da 2016.
Kuma wannan shine karo na ukku, da kungiyar ta Najeriya, ke doke kungiyar kasar Kamaru, a wasan karshe.
Your browser doesn’t support HTML5