Najeriya na fuskantar kalubalen wucewa wasan samun gurbin gasar kasashen Afirka, bayan da kasar Togo ta lallasa ta da ci 4 da 1 tun a zagayen farko na gasar a filin wasan Stade Kegue ranar lahadi.
Super Eagle ta fara wasan cikin nasara, yayin da a minti goman farko dan wasanta Ibrahim Sunusi ya zura mata kwallo, ana tafe ne Togo ta rama a minti na 16 ta hanun Richard Nane.
Bayan dogon wasa ne Nane daga Kasar Togo ya kara kwallo daya a wajajen mintuna na 67. Tchakei Marouf ne ya zura kwallo na 3 a minti na 75, yayin da Agoro Ashraf ya zura na 4 ana daf da tashi.
Super Eagles wanda a 2018 ta kai har zagayen karshe gasar Afurka da aka yi a Moroko, a yanzu tana bukatar yin nasara a zagaye na biyu da a kalla kwallaye 3 wanda babu ramawa, wanda za a yi a Najeriya. Haka ne kawai zai bata damar tsallakewa zuwa gasar da za a yi a Kamaru a 2020.