Super Eagles Zasu Yi Rawar Gani

'Yan Wasan Super Eagles

An bukaci ‘yan wasan kungiyar Super Eagles dasu sa kaimi a wasan da zasu yi da Guinea, a kasar Rwanda, a rukunin “C”.

Ministan Matasa da wasani Barrister Solomon Dalung, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya bada inda ya yabawa ‘yan wasan kan kokarin su na yin kunnan doki da kasar Tunisia, a ranar juma’ar da ta gabata.

Yace kungiyar sun nuna karamci da hazaka da kuma jajircewa a wasanin su duk da kalubalen da suka fuskanta. Amma a cewar sa yasan ‘yan wasan zasu yi rawar gani a wasansu da Guinea, a yau din nan.

Ya kuma yi alkawarin cewa zai tabbatar da ganin cewa sun sami duk abunbuwan da ya cancanci su samu.

Ya Kara da cewa ‘yan Najeriya, na taimakawa da adu’ar nasara.