Sunday Oliseh Ya Yada Kwallon Mangwaro...Domin Ya Huta Da Kuda

Sunday Oliseh ya ajiye mukaminsa na kwach din ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, a bayan da yace hukumar NFF ta keta haddin kwantarakinsa, sannan ta ki tallafawa a karawa mai muhimmanci da ‘yan Super Eagles zasu yi da Masar a wata mai zuwa a wasannin share fagen cin kofin kwallon kasashen Afirka na 2017.

Ran 25 ga watan Maris a Kaduna ne Najeriya zata karbi bakuncin ‘yan Masar, wadanda sau 7 suna lashe kofin zakarun kasashen Afirka, wadanda kuma sune ke saman wannan rukuni nasu. Kasar da take sama a kowane rukuni ne kawai take da tabbas na hayewa zuwa ga Gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2017 da za a yi a kasar Gabon.

Wani babban jami’in hukumar ta NFF ya fada yau jumma’a cewa Oliseh yayi murabus a bayan da ya kasa samun irin goyon bayan da yake bukata daga hukumar.

Jami’in yace Oliseh ya kuma koka kan yadda aka keta haddin kwantarakinsa sau da dama. Oliseh yace watanni hudu ke nan yanzu ba a biya shi albashinsa ba, haka kuma ba a samar masa da gida ko masauki a Abuja kamar yadda aka yi alkawari karkashin kwantarakin nasa ba.

Haka kuma an ce Oliseh bai ji dadin korari mataimakinsa, Tijjani Babangida, da hukumar NFF ta yi ba, da kuma rade radin cewa ita hukumar ta tuntubi tsohon kwach na Cote D’Ivoire, Herve Renard, wanda a yanzu ya karbi ragamar kwach na kasar Morocco.

An nada tsohon kyaftin din na ‘yan wasan Najeriya, Oliseh, a zaman kwach a watan Yulin 2015 domin maye gurbin Stephen Keshi da aka kora.

Amma tun daga lokacin sai dangantaka a tsakaninsa da hukumar NFF ta yi tsami, musamman a bayan da aka yi waje rod da Najeriya tun a zagayen farko na gasar cin kofin kasashen Afirka da aka yi a kasar Rwanda kwanakin baya.