Yayi da jami’an tsaro ke ci gaba da farautar wadanda suka sace tsohon sakatren Gwamnatin Najeriya, Olu Falae, wanda kuma shine shugaban jam’iyyar SDP,’yan majalisar tarayya da na jahohi, ‘ya’yan jam’iyyar SDP, sun bukacin shugaban Muhammad Buhari da ya gaggauta daukan matakin ganin an ceto tsohon sakataren Gwamnatin Najeriyan.
A wajan wani taron manema labarai a Yola fadar jahar Adamawa, dan majalisar wakila dan jam’iyyar ta SDP, Kwama Lawuri, ya bayana takaicin shi kan sace shugaban jam’iyyar da yanzu ya shafe kwanaki ba’a san inda yake ba.
Kuma kamar yadda bayanai ke nunawa wadanda su kayi garkuwa da tsohon sakataren Gwamnatin tarayyan Olu Falae, na neman Naira miliyan 100, a matsayin kudin fansa.
Dan majalisan wakilan yace abun takaici ne sace wannan dattijo mai kimanin shekaru 77, a gonar sa Ila ojo, dake Akure, ta arewa a jahar Ondo, dan haka suka bukaci shugaba Buhari, daya dauki matakin da yakamata akan yadda ake garkuwa da mutane ana neman kidin fansa.
Ita ma a nata tsokacin ‘yar majalisar dokokin jahar Adamawa kuma shugaban marasa rinjaye, Justina Obadia Kom, ta nuna takaici game da yadda ake samun yawaitar garkuwa da mutane ana neman kudin fansa.
Your browser doesn’t support HTML5