To sai dai Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayyar Aminu Waziri Tambuwal, a lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa a matsayin gwamnan Jihar Sokoto, yayi kakkausar suka akan lamarin, wanda yace ya sabawa kundun tsarin mulkin Najeriya.
Tambuwal yace “ina so in shaida muku cewa, babu wani abu makamancin gwamnatin rikon gadi a tanade-tanaden kundun tsarin mulki. Zabin da kawai ake da shi shine shirya zabe sahihi bisa adalci.”
“Ai wannan suna jin tsoro ne, domin kuwa ina da yakinin cewa, jam’iyyar APC ce zata kafa gwamnati mai zuwa idan har aka gudanar da zabe.”
Taron kaddamar da dan takarar a Sokoto, wanda ya samu hallartar shugaban jam’iyyar na kasa Chief John Oyegun, da Bola Ahmed Tinubu da ma gwamonin Kwara da Edo, ya mayar da hankali ne akan halin da Najeriya take ciki na tabarbarewar al-amura, abunda gwamnan Jihar Adams Oshiomole yace ya kai halin “La Haula”.
“A yanzu, zabe da za’a yi, babu maganar kai daga ina kake. Abunda yake kasa shine, wane ne zaiyi aiki da gaskiya, a gani cewa idan talaka ya kwanta bacci ya tashi, baya jin tsoro”, a cewar Oshiomole.
Your browser doesn’t support HTML5