Sule Lamido ya kare zaben Modu Sherif a matsayin shugaban PDP

Sanata Ali Modu Sheriff sabon shugaban PDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya kare zaben Sanata Ali Modu Shariff a matasayin sabon shugaban PDP a firar da ya yi da Muryar Amurka

Sule Lamido yace akwai umurnin kotu kuma tunda an samu gurbi dole ne a cike ba sai kotu ta bada umurni ba.Wannan yana cikin tsarin jam'iyyar.

Akan wai Modu Shariff sabon shiga PDP ne sai Sule Lamido yace mutane suna da 'yanci su fasara fahimtarsu da lamarin, wato nada wanda ya shiga jam'iyyar kwana kwanan nan a matasayin shugaba. Yace 'yancinsu ne.

Amma abun lura nan shi ne ba zaben gama gari aka yi ba. Cewa aka yi wani bangaren kasar ya zabi shugaba ya kawo. Wanda yankin ya kawo shi aka zaba. Yace lokacin da aka yi jam'iyyar hadin gambiza ta APC wadanda suka shigeta a watan Nuwamba sun tsaya zabe watan Maris, tuk cikin wata uku aka basu takara. A wancan lokacin mutane basu yi korafi ba saia zaben Modu Shariff.

Akan wai ana kallon Modu Shariff da wasu zargi Lamido yace duk Najeriya ana yiwa 'yan PDP zargin kazanta amma sun shiga APC duk abun da suka yi kuma ya zama halal. Amma zaben Modu Shariff ya zama haram.

Duk kuri'un da APC ta samu daga jihohi daban daban na PDP ne. Abun da ya tabbata yanzu shi ne APC ta firgita da zaben Modu Shariff. Suna tsoronsa. Idan ya koma APC shi lafiyayye ne amma tunda yana cikin PDP haramtace ne.

Akan cewa PDP zata fitarda dan takaranta daga arewa sai ya ce ai lokacin zabe bai yi da za'a soma batun dan takara. Idan lokacin ya yi aka fitar da dan takara daga arewa to sai a sake shugaban jam'iyyar.

Ya kara da cewa 'yan APC ga dodo nan ya fito masu gudu su gudu. Shi ne baya tsoron kowa a APC kuma sun sanshi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sule Lamido ya kare zaben Modu Sherif a matsayin shugaban PDP - 5' 07"