A Janhuriyar Nijar an gudanar da wasan yara na kasashe biyar masu amfani da harshen Faransanci da su ka hada da Nijar da Ivory Coast da Mali da Burkina Faso. Wasan, wanda ake kira ‘SUKABE,’ wanda aka gudanar a birnin Damagaram, ya hada da wasan kwaikwayo da barkwanci da nuna al’adu da gabatar da kasidu da kuma bayyana ma matasa ‘yancinsu da hakkokinsu.
Shugaban shirin na SUKABE, Soumana Tinni Wonkoye ya ce makasudin shirya wasan na SUKABE ya hada da ganin cewa matasa bas u mance da al’adunsu na gargajiya ba, da kuma fadakar da jama’a a daina bugun yara barkatai da hana su zuwa makaranta da kuma, wannan ya kuma hada da kai yaran wasu muhimman wurare.
Su ma yara mahalarta wasun sun bayyana muhimmancin shirya shi da cewa wasa da dariya da raye-rayen da ake yi sun burge su tare kuma da fayyace masu wasu muhimman abubuwa, musamman bayan ziyarar wasu garuruwa:
Your browser doesn’t support HTML5