Sojojin Sudan sun koma kan filayen noman dake kan iyaka da Habasha a ranar Alhamis kana suka baza kan su a kan yankin kasar da ‘yan bindigan Habashan suka kwashe sama da shekaru 25 suna rike da iko wurin, a wani dadadden rikici tsakanin Khartoum da Addis Ababa.
Kungiyar ta ‘yan bindigan Habasha suna kiran yankin Shefta mai yawan harkoki a lokacin rani na kowace shekara, suna satan amfanin gona a Fashaqa da wasu unguwanni da Sudan take da’awar nata ne.
Wani jami’in tsaron yankin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya fadawa Muryar Amurka cewa sojojin Sudan sun kwace ikon yankin.
Sudan tana daukar nauyin ‘yan gudun hijiran Habasha da suka arce daga yakin Tigray da ya barke a cikin watan Nuwamba tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ‘yan bindigan Tigray ta Tigray People’s Liberation Front (TPLF), a takaice.
Sama da ‘yan gudun hijira dubu 43 ne aka karkasa su zuwa sansanoni a biranen Sudan guda biyu da suka hada da Qadarif da Kassala.
Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta ‘yan gudun hijiran zasu kai dabu dari nan da ‘yan makwanni masu zuwa.