Sudan Ta Kudu Ta Janye Daga Tattaunawa a Kasar Habasha

  • Ibrahim Garba

Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir

Yayin da ake harmar fara wani zagaye na tattaunawa tsakanin bangarorin da ke fada a Afirka Ta Kudu, sai gashi gwamnatin kasar na cewa sai dai a canza kasar da za a yi tattaunawa ta gaba.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce ta na so a yi wata ganawa tsakanin Shugaba Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar, to amma ba a cikin wata kasar da ke kuryar Afirka, ko kungiyar IGAD ba.

Da an shirya cewa da Kiir da Machar za su gana a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha a ranar 20 ga watan Yuni. To amma da ya ke magana da 'yan jarida jiya Jumma'a, mai magana da yawun gwamnatin Sudan ta Kudu Michael Makuei ya bayar da shawarar a kai taron a kasar Afirka Ta Kudu.

Machar, wanda tsohon Mataimakin Shugaba Kiir ne, ya yi hijira zuwa Afirka Ta Kudun a 2016, bayan da yarjejjeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da bangaren Machar, wadda ake kira SPLM-IO, ta rushe.

Makuei ya ce kasashen kungiyar IGAD uku, wato da Sudan da Kenya da Habasha, na gasar daukar nauyin wannan taron saboda wasu manufofi. "Abin da ya fi fa'ida shi ne gudanar da taron a wata kasa ta dabam, saboda kar wata daga cikin kasashen nan uku, ta yi amfani da taron wajen wani abu face batun zaman lafiya.