Sudan ta Kudu Na Gaf da Fadawa Yakin Kare Dangi -MDD

Sansanin 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu dake cikin Uganda

Yau Jumma'a ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD zai kada kuri'a kan ko ya azawa Sudan ta Kudu takunkumin hana sayarwa kasar makamai.

Amma jakadu sun ce kudurin da Amurka take jagoranta sai tayu ba zai sami nasara ba, duk kashedin da aka yi cewa sabuwar kasar tana daf da fadawa ga yakin kare dangi.

Amurka wacce kasashen Birtaniya da Faransa suke goyawa baya, sun dage cewa akwai bukatar a gaggauta dakile kwararar makamai zuwa kasar domin kaucewa ci gaba da zubda jini a kasar da yaki ya daidaita.

Amma Rasha, da China, da Japan, da Malysia, da Venezuela,, kuma masu muhimmanci kasashen Afirka uku dake kwamitin sulhun, da Angola, da Masar, da Senegal, duk sun bayyana shakku sosai kan matakin.

Wannan turjiyar tana zuwa ne duk da gargadin da babban sakataren na MDD Ban ki-moon ya bayar a farkon makon nan cewa, Sudan ta Kudu ta tasamma fadawa yakin kare dangi muddin ba’a dauki matakin gaggawa ba na azawa kasar takunkumin hana a saida mata makamai ba.

Yara da rikicin Sudan ta Kudu ya raba da iyayensu