Sabon Mataimakin Shugaban Kasa Na Daya na Sudan Ta Kudu, Taban Deng Gai, ya ce kasar na cikin abin da ya kira "kwanciyar hankali da lumana" kuma ta na cigaba da sauye-sauye, bayan tashe-tashen hankulan da su ka auku a Juba, babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 300 a watan jiya.
WASHINGTON D.C —
Deng ya yi magana da 'yan jarida a birnin Nairobi jiya Laraba, yayin da ya je don ganawa da Shugaba Uhuru Kenyatta. Ya zargi 'yan jarida da ba da rahotannin karya cewa an cigaba da yaki a Juba da sauran wurare.
An cimma wata yarjajjeniyar kwance damara hakanan a Juba, tun bayan tashin hankalin da aka yi a watan Yuni, to amma an yi ta samun rahotannin fadace-fadace a yankin Equatoria, da kuma yankin da ke cikin tsohuwar jahar Bahr el-Ghazai Ta Yamma tsakanin dakarun da ke goyon bayan Shugaba Salva Kiir da masu goyon bayan mai adawa da shi Riek Machar.
Deng ya ce gwamnati ta kuduri aniyar hada kan dakarun su zama guda, da zummar kammala hada kan sojojin zuwa watan Mayun 2017.