Jakadan kasar Sudan ta Kudu a Amurka, Gordon Buay, ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta sake tunani kan janye taimakon da take ba kasarsa saboda acewarsa, yin hakan zai shafi shirin zaman lafiya a kasarsa.
WASHINGTON DC —
Wani babban jami’in diplomasiyar Sudan ta Kudu a Amurka ya yi kira ga Amurka da ta sake tunani kan shirin janye taimako da take bai wa Sudan ta Kudu.
A cewar Gordon Buay, hakan wani koma baya ne ga shirin samun zaman lafiyar kasar.
Jakada Buay, babban jakadan Sudan ta Kudu a Washington, ya fada cewa sanarwar da fadar White House ta fitar a shekaranjiya Talata da kakkausar kalamai a kan Sudan ta Kudu ka iya yin mummunar tasiri.
Ya kara da cewa wannan mataki zai aike da sakon da zai haifar da rashin fahimta ga 'yan tawayen kasar.