Sudan Ta Cimma Yarjejeniya Tsakaninta Da Kungiyoyin 'Yan Tawaye

  • Ibrahim Garba

Janar Mohamed Hamdan Dagalo (tsakiya) yayin sa hannu kan yarjejniyar.

Gwamnatin Sudan da kungiyoyin ‘yan tawaye sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da tarihi.

Wannan dai ya kasanace wani muhimmin mataki na farko wajen kawo karshen yakin da aka shafe shekaru 17 ana tafkawa, a cewar wani wakilin kafar labarai ta AP.

Shugabannin Kungiyar Juyin Juya Halin Sudan ta (SRF), wacce hadaka ce ta kungiyoyin ‘yan tawayen yankin Darfur da ke yammacin kasar, da kuma jihohin Kordofan da Blue Nile (ko al-Nil al-Azrag) da ke kudancin kasar, sun daga hannayensu sama don nuna farin cikinsu, bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Yarjejeniyar, wacce aka cimma a Juba, babban birnin kasar Sudan Ta Kudu , an sa hannu akai amma, kamar yadda aka fassara, “ba a ida rattabawa ba,” lafazin da aka yi amfani da shi, don nuna cewa kofa na nan bude ga wasu kungiyoyi biyu muhimmai, wadanda har yanzu ke jan kafa, su samu damar shiga yarjejeniyar don a kammala ta, a cewar jami’ai.