A yau Lahadi, gwamnatin Mulkin Soji da gamayyar shugabannin masu zanga zanga a Sudan, sun kaddamar da wani shiri na raba mukamai a gwamnatin wucin gadi da za a kafa.
A ranar 17 ga watan nan na Agusta, ake sa ran bangarorin biyu za su rattaba hannu kan kundin tsarin mulkin da zai ba da damar aiwatar da wannan hadaka.
Ana fatan, kwana guda bayan rattaba hannun, za a ayyana majalisar mulkin gwamnatin ta wucin gadi, wacce za ta tafiyar da ragamar mulkin kasar har na tsawon shekaru uku.
Sannan a ranar 20 ga watan nan, za a ayyana Firai Minista, daga bisani kuma sai a ayyana sunayen ministocin gwamnatin.
Kasar ta Sudan ta shiga rudanin siyasa a ‘yan watannin nan, inda aka fara zanga zanga a watan Disambar bara, kan tsadar man fetur, lamarin da ya sa masu zanga zanga suka nemi sauyi, duk ko da cewa sojojin kasar sun kifar da gwamnatin tsohon shugaba Omar Al Bashir.