Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka, Malama Hilary Clinton, take gabatarda jawabin fatar laheri ga Nigeria dake bikin samun mulkin kanta

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka, Malama Hilary Clinton, take gabatarda jawabin fatar laheri ga Nigeria dake bikin samun mulkin kanta

<a href="http://www.voanews.com/hausa/news/special-reports/politics/Nigeria-50h-Anniversary-Celebration-104208999.html"> http://media.voanews.com/images/nigeria-50-480.jpg

A madadin Shugaba Obama da mutanen Amurka, I na farin cikin taya yan Nigeriya murnar zagayowar ranar samin yancinsu karo na 50.

A lokaci irin wannan, mukan girmama tarihin Nijeriya, da cigaban da ta samu, da kuma jagorancin da ta ke yi ba kawai a Yammacin Afirka ba, amman har a fadin Nahiyar Afirka da ma Duniyar baki daya. I na so musamman, in yaba da rawar da Nijeriya ta taka wajen kawo kwanciyar hankali a wuraren da ke fama da tashe-tashen hankula, ta wajen gagarimin gudunmowarta a sojojin kiyaye zaman lafiya.

Nijeriya da Amurka na da dangantaka na kud-da-kud, wanda ya bayyana barobaro a kwamitin Amurka da Nijeriya da mu ka kaddamar wannan shekarar. Ta wannan kwamitin, kasashen namu sun karfafa hadin kanmu kan batutuwa da dama, wadanda su ka hada da shugabanci na gari da kuma gaskiya da rikon amana, da makamashi, da batun tsaro a yankuna, da kuma wanzar da zaman lafiya da cigaba a yankin Niger Delta. Ta wajen hadin kai, za mu iya samin cigaban da ya ma wuce wannan.

Wannan lokaci ne mai muhimmanci ga Nijeriya. Zaben shekara mai zuwa wata dama ce na karfafa dimokaradiyyar Nijeriya a sa'ilinda ku ke kara jaddada aniyarku ta samar da ingantaccen shugabanci da kuma tsarin tafi da mulki bisa kundin tsarin mulki. A matsayin Amurka na abokiyar huldarku za ta taimaki Nijeriya wajen gudanar da ingantacce, kuma karbabben zabe a yanayin kwanciyar hankali. Kuma za mu cigaba da hada kai da Nijeriya don mu sami makoma mai kyau ga yan kasashen na mu biyu.

Don haka, bari in sake yi wa yan Nijeriya fatan shagulgula cika shekaru 50 da samin yancin kai cikin farin ciki da annashuwa.