Speto Janar Na 'Yansandan Najeriya Yace Zasu Yi Maganin Boko Haram

Rundunar 'Yansandan Najeriya a faretin da suka yi a bikin rnatsarda sabon shugaban kasa.

Speto Janar na 'yan sandan Najeriya Alhaji Hafiz Ringim ya baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa nan da mako daya zuwa biyu,rundunar zata murkushe 'yan Boko haram

Rundunar 'yansandan Najeriya tayi alkawarin zata magance matsalar 'yan boko haram nan da mako daya zuwa biyu. Babban Speto janar na 'yansandan Najeriya Alhaji Hafiz Ringim ne ya bayyana haka a hira da yayi da wakilin Sashen Hausa na Muriyar Amurka a yankin Niger Delta.

Alhaji Hafiz Ringim yace karuwar tashe tashen hankula kama daga fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran laifuffuka ya zama ruwan dare gama duniya. Sabo da haka Najeriya ba zata zama daban daban ba.Duk da haka Alhaji Ringim yace gwamnatin Najeriya tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta tabbatar da tsaro.

Babban Speto janar din, yace ganin yanzu an kammala zabe da rantsar da sabbin shugabanni, rundunarsa zata dukufa wajen "raba zare da abawa",watau zatayi tankade da rai-raya,domin sallamar duk wani dansanda bata gari.

Da yake magana kan zargi da aka yi masa a kafofin yada labarai cewa ya nemi hana jami'an EFCC kama tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya Mr. Dimeji Bankole,Mr Ringim yace babu kanshin gaskiya a labarin