Son Zuciya Annobar Duk Jam'iyyu Najeriya Ce

Sule Lamido, gwamnan Jihar Jigawa

Harkar siyasar Najeriya ta dauki wani sabon salo mai daure kai yayin da 'yan siyasa na barin jam'iyyunsu suna shiga wasu.
Ga bisa alamu jam'iyyu mafi karfi a Najeriya wato PDP da APC sun shiga galari na shigowa da ficewar wasu gaggan jam'iyyar a daidai lokacin da shugabannin jam'iyyun ke kokarin yi masu garanbawul domin su dadaita alamuransu.

PDP dai ta fuskanci ficewar wasu gwamnoni guda biyar zuwa APC yayin da wasu gaggan APC suka fice zuwa PDP lamarin da Sule Lamido ke ganin tun farko annoba ce ta shiga PDP kana ta yadu zuwa wasu jam'iyyu. Ya ce kodayake Bamanga ya tafi amma abun annoba ne kuma yana cikin kowace jam'iyya. Ya ce duk koina akwai wannan tsarin son zuciya da son biyan bukatun kai. Mutane na son a yi abun domin su samu ba domin a yi gyara ba.

Alhaji Ahmadu Mu'azu ya hau kan kujerar shugabancin PDP amma aikin yana da wuya. Sule Lamido ya cigaba da cewa mutum ya tsaya ya tambayi kansa meye Najeriya. Duk abun da mutum zai yi ya tabbatar ya kare matsayin Najeriya da kwarinjininta. Ya ce babu laifi a ce kai yaron wani ne amma dai maganar ita ce kana da mutunci a matsayinka na da. Ya ce ya zanta da sabon shugaban PDP wanda shi ma tsohon gwamna ne. Ciwon zuciya da bakin ciki suka sa wasu tsoffin gwamnoni da wadanda ke ci yanzu suka fita daga PDP. Idan ba haka ba yaya mutum zai tashi ya bar gidansa ya je gidan wani. Ya ce abun bakin ciki ne.Da can an yi abubuwa babu ka'ida. Ya gargadi sabon shugaban ya fito fili ya fadi duk kurakuran da aka yi a karkashin Bamanga Tukur kamar korar Oyinlola da Baraje da Amaechi da sauransu. Duk abubuwan da aka yi da suka sabawa tsarin PDP ya fadesu. Idan ya yi hakan zai shafawa zuciyar wadanda aka saba ma ruwan sanyi.

Mataki na biyu kamar yadda Sule Lamido ya ce shi ne a ga yadda za'a shawo kan mutanen da aka saba masu.

To amma Alhaji Umaru Diembo tsohon ministan mai a Najeriya kuma kusa a jam'iyyar APC ya ce babu hujja da zat a sa wasu su fice daga jam'iyyar wai domin ba'a tuntubesu ba domin suna ganin cewa sun bada babbar gudunmawa lokacin kafa jam'iyyar. Ya ce ana taruwa ne a yi yawa a yi karfi domin a kwace mulki daga shegiyar uwa PDP. Ya ce sun shigo jam'iyyar ne domin rayar da kasar ko domin cimma muradun kansu?. Yana ganin basu da hujjar barin APC kuma yin hakan ma tamkar yada girma ne.

Your browser doesn’t support HTML5

Son Zuciya Annobar Duk Jam'iyyun Najeriya Ce-5:30