Gwamnatin Somaliya ta ce za ta bayar da lasisin hako mai ga kamfanonin kasashen waje, duk kuwa da kiraye-kirayen ‘yan adawa cewa a jira har sai an bullo da ka’idoji da kuma dokokin tafi da bangaren mai na kasar.
Binciken karkashin kasa da wasu kamfanonin Burtaniya biyu su ka yi, wato da Soma Oil & Gas da kuma Spectrum Geo, ya nuna cewa kasar Somaliya na da arzikin mai a ta bakin gabarta da tekun Indiya, a tsakanin biranen Garad da Kismayo. Adadin mai da ke wajejen na iya kai wa ganga biliyan 100.
Gwamnatin dai ta ce za ta saurari masu takarar samun lasisi a ranar 7 ga watan Nuwamba, kuma nan take za a sanar da wadanda su ka yi nasara. Ta ce za a rattaba hannu kan yarjajjeniyar raba ribar a ranar 9 ga watan Disamba, ta yadda kuma za a fara aiwatar da yarjajjeniyar ranar 1 ga watan Janairun 2020.