Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, yace jihar tana hasarar Naira Milyan 360 ako wani wata, ta hanyar ma'aikatan bogi, da kuma ma'aikata da aka dauka amma kuma ake ragewa albashi.
Gwamna Tambuwal, ya fadi haka ne lokacin da yake kaddamar da bikin sayar da takin zamani a jihar. Gwanan yace an dauki wasu ma'aikata wadan da ake biyan kashi 40% cikin dari na albashi, saura kuma su shiga aljihan shugabanni.
Rukunin zambatar na biyu kuma, shine ta daukan ma'aikatan bogi, wadanda kudaden suke tafiya aljihan shugabannin kananan hukumomin da mukarrabansu.
Duk kokarin da wakilin Sashen Hausa Murtala Farouk Sanyinna yayi, domin samun karin bayani kan matakan da gwanatin take shirin dauka domin shawo kan lamarin, daga Gwamnan ko gwamnatinsa ya ci tura.
Amma da ya tuntubi wani tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa, Abdulahi Mu'azu Hassan, ya tabbatar da sace sacen. Yace al'amarin ya hada harda shugabannin jam'iyun siyasa da sauransu.
Daga nan ya bada shawarar hanyoyi da yake gani idan aka bi zasu taimakawa wajen rage ko hana sace sacen baki daya. Wadannan sun hada da barin talakawa su zabi shugabanninsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5