Al’umar jihar Sokoto ta shiga cikin yanayin juyayi a kwanakin nan saboda yawaitar mace-macen jama’a a sassa daban daban da jihar ke fuskanta.
Akasarin wadanda suka rasa rayukansu masu yawan shekaru ne, ko da yake akwai masu matsaikatan shekaru a cikinsu.
Malam Maina Sambo, mazaunin jihar Sokoto, ya ce ko a safiyar ranar Litinin 4 ga watan Mayu sun binne mutum 17.
A cewa Labaran Sahabi, daya daga cikin ma’aikatan da ke gina kaburbura a makabatar Tudun Wada da ke cikin birnin Sokoto, ya bayyana mace-macen a matsayin annoba.
Ya kuma danganta lamarin da yanayin zafi da ake yi a bana. A cewarsa, an taba fuskantar wannan bala’in shekaru biyu da suka gabata.
Abubakar Suleiman Uban Doman Gwado, dan majalisar Sarkin Musulmi mai kula da harkokin makabartu, ya ce ba shakka wannan wani abu ne mai ta da hankali saboda daga ranar Juma’a 1 ga watan Mayu zuwa yanzu, sama da mutane 200 suka mutu a jihar.
Wasu na ganin yawaitar mace-macen ba zai rasa nasaba da cutar coronavirus da ta game duniya baki daya ba.
Dr. Abubakar Suleimane, kwamishinan Lafiya na jihar Sokoto kuma shugaban kwamitin kula da cutar coronavirus a jihar, ya ce an kafa kwamitin ne don yin bincike akan duk bayanan da aka samu kuma za a kwatanta alkaluman mace-macen shekarun baya a lokacin yanayin zafi da na wannan karon.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Muhammadu Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5