An samu arangama tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Rumjin Kalmalao da ke cikin karamar hukumar Illela ta jahar Sokoto, mai tazarar kilomita biyu daga birnin Konni na Jamhuriyar Nijar.
Rahottani sun bayyana cewa Fulani makiyaya da Manoman sun yi amfani da makamai da suka hada da bindigogi a lokacin rikicin.
Mutum biyu ne suka rasa rayukkansu, ya yin da wasu da dama suka raunata.
Muhammadu Kane, dake zaman hakimin garin kuma daya daga cikin wadanda suka raunata sanadiyar rikicin, ya fadawa Muryar Amurka cewa rundunar tsaron jihar Sokoto ta yi kokarin dawo da zaman lafiya a yankin ta hanyar aikawa da dakarunta.
Kwamishinan Yan Sandan jihar, da makarrabansa sun kai ziyara yankin domin ganewa idanunsu abin da ya faru.
Lamarin dai ya haifar da zaman dar-dar tare da fargabar kada rikicin ya shafi makwabtansa.
Ga karin bayani a sauti daga wakilinmu Harouna Mamane Bako.
Your browser doesn’t support HTML5