Lamarin dai ya faru ne a garin Tudun Doki na karamar hukumar Gwadabawa dake gabashin Sakkwato, a arewa maso yammacin Najeriya.
Garin na Tudun Doki, gari ne da ya hada Hausawa da fulani zaune wuri daya, kuma Fulanin ne suka soma jin karar harbe-harben kafin kowa ya ankara, a cewar Kantoman karamar Hukumar Muhktar Bello Abdulrahman.
Zama irin na Hausawa da Fulani wuri daya zama ne wanda duk lokacin da aka samu harin ta'addanci, za'a rika kallon kallo, kuma a kan haka ne Kantoman karamar hukumar yace suka zauna da jama'ar yankunan suka tattauna.
Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta hannun kakakin ta a Sakkwato ASP Ahmad Rufa'i ta tabbatar da mutuwar mutane shida, sanadin wannan harin, sai dai yace suna ci gaba da bincike a kan batun.
Ku Duba Wannan Ma Sojoji Sun Ce Sun Halaka 'Yan Ta'adda Bakwai A Kaduna, Sun Kwato Makamai Da DamaWannan lamarin dai yana faruwa ne a daidai lokacin da daruruwan jama'ar da ayyukan ta'addanci suka raba da muhallansu, ke ci gaba da fuskantar kalubalen rayuwa.
Gwamnatin jihar Sakkwato kamar takwarorin ta na jihohin arewa maso yamma na ci gaba da daukar matakan shawo kan wannan matsalar ta ayyukan 'yan bindiga, sai dai lamarin na ci gaba da wanzuwa a wasu wurare.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5