Sokoto: Kotu Ta Saka Ranar Fara Sauraron Shari’ar EFCC Da ‘Yan Kasar China Biyu

EFCC Ta Gurfanar Da Yan Kasar China Biyu Gaban Kotu

Babbar kotun jihar Sokoto karkashin jagorancin babban Alkali Muhammad Sa’idu Sifawa ta saka ranar 15 ga watan Yuni domin fara sauraren shari’ar ‘yan kasar China biyu da hukumar yaki da al’mundahana EFCC ta gurfanar.

Hukumar EFCC ta gurfanar da mutanen biyu ‘yan asalin kasar China gaban kotu ne akan zargin aikata laifuka biyu da suka hada da bayar da toshiyar baki ga jami’in gwamnati da kuma hada baki wajen aikata ba daidai ba.

Mutanen biyu da ake zargin aikata laifukan Meng Kun da Xu Koi, sun ‘ki amincewa da aikata laifukan lokacin da Alkali ya tambayesu. Akan haka ne lauyan masu shigar da kara ya bukaci kotun ta saka ranar da za a fara sauraren karar, inda aka saka ranar 15 ga watan Yuni.

EFCC Ta Gurfanar Da Yan Kasar China Biyu Gaban Kotu

Shi kuma lauyan dake kare wadanda ake zargin ya nemi Alkalin kotun ya bayar da belin Meng da Xu, inda Alkalin ya amince da hakan amma sai ranar 18 ga wannan watan za a bayar.

Kamar yadda lauyan hukumar EFCC, Isah Maila Gwani, ya shaidawa Muryar Amurka, tun farko dai an kama wadanda ake zargi ne bisa yunkurin baiwa babban jami’in hukumar EFCC cin hanci na kudi, kan wani bincike da ake yi akansu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Muhammad Nasir daga Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Sokoto: Kotu Ta Saka Ranar Fara Sauraron Shari’ar EFCC Da ‘Yan Kasar China Biyu – 3’17”