A jihar Sokoto har yanzu ana cigaba da samun kalubale dangane da turjiyar iyaye akan kin amincewarsu da ba 'ya'yansu allurar rigakafin cutar shan inna.
A jihar bincike ya nuna cewa an sami kimanin gidaje 2900 da suka ki yadda a digawa 'ya'yansu allurar rigakafin cutar shan inna yayinda ake bada allurar a watan Oktoban da ya shige..
Irin wannan lamarin na Sokoto ya zaburar da masu ruwa da tsaki dangane da kawar da cutar kama daga hukumomi har zuwa hukumomin bada tallafi domin ganin a shawo kan matsalar. Suna ganin ya kamata a kaddamar da wani zagayen bada allurar na musamman a wannan watan na Disamba.
Dr Aminu Shehu shi ne daraktan cututuka masu yaduwa da rigakafi na hukumar kiwon lafiya a matakin farko a jihar Sokoto yace gwamnati tana kokari. Kodayake an fitar da kasar daga ayarin kasashen dake da cutar akwaita amma za'a cigaba da yakarta nan da shekaru biyu. A wannan shekarar yace an yi zagaye takwas duk a kokarin kakkabe cutar.
Kan kalubalen da suke samu daga wasu iyaye Dr Shehu yace ana bin jama'a sannu a hankali ana tattaunawa dasu tare da kara wayar masu da kawunansu. Idan aka cigaba da yin hakan za'a samu nasara.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5