Baya ga soke zaben kujerar Dan Majalisar Tarayya da APC ke kai a Gombe, jam’iyyar ta sake gamuwa da wata matsala ta hana ta shiga zaben da za a sakena kujerar Dan Majalisar Wakilan na Karamar Hukumar Akko ranar 19 ga watan Disamban wannan shekarar.
Sakataren Mulki a Hukumar Zaben Jahar Gombe Mr. Gregory Tukumbor y ace umurnin hana jam’iyyar APC shiga zaben da za a sake din ya fito ne daga Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Yola. Hasali ma, in ji shi, lokaci ya wuce APC ba ta gabatar da takardun shirin shiga zaben ba. To amma dan takarar da kotun ta soke zabensa, Alhaji Umaru Barambu y ace shi fa zai shiga zaben saboda abin da kotun ta ce kawai shi ne bai bi ka’ida ba lokacin da ya fice daga jam’iyyar PDP. Barambu y ace zai yi takarar ce karkashin APC.
To amma kakakin jam’iyyar APC a jahar Gombe, Mr. Bili Garba y ace abin da su ka sani shi ne kotu ta hana Barambu ne tsayawa takara amma ba APC ba. Saboda haka jam’iyyar APC za ta shiga takarar.
Ga wakilinmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5