A yau Laraba Sojojin kasar Zimbabwe sun ce ba hambarar da gwamnatin kasar suka yi ba, suna masu cewa dadadden shugaban kasar Robert Mugabe da iyalansa suna nan cikin koshin lafiya.
“Muna bibiyan bata-gari ne kawai da ke zagaye da shi, wadanda suka aikata laifukan da ke kawo cikas wajen gudanar da al’amuran yau da kullum da na tattalin arziki a kasarmu, domin mu gurfanar da su a gaban kuliya.” Inji wata wata sanarwa da sojoji suka fitar ta kafar talbijin.
Wannan sanarwa ta biyo bayan rahotannin da shaidu suka bayar na cewa an samu fashewa har guda uku da kuma harbin bindiga mai karfi a Harare, babban Birnin kasar ta Zimbabwe da safiyar yau Laraba.
Har ila yau shaidu sun ce sun ga motocin sojoji da dakarun kasar akan tituna da safiyar yau Laraba, sa’oi bayan da sojojin suka karbe ikon gidan talbijin din kasar na ZBC.
Al’umar kasar sun ce a maimakon su kalli labarai da karfe 11 dare, sai aka yi ta saka wakokin na bidiyo.
Wani kakakin Ofishin jakadancin Amurka a birnin na Harare, ya fadawa Muryar Amurka cewa babu wata alamar tarzoma a daren jiya Talata zuwa wayewar gari yau Laraba, sannan bai tabbatar da kasancewar motocin sojoji akan tituna ba.
Ofishin jakadancin na Amurka ya yi gargadi ta kafar yanar gizonsa ga Amurkawa, da su zauna a gidajensu su yi aiki daga gida.
Bayan kuma da aka zauna cikin zullumin ko dakarun kasar sun karbe ikon gidan talbijin din kasar na ZBC ne, sojojin sun tabbatar da cewa suke tafiyar da ragamar al’amura.
A wata sanarwa da suka watsa kai-tsaye daga hedkwatar gidan talbijin din na ZBC, Manjo Janar Sibusiso Moyo, ya ce abinda ya faru ba juyin mulki ba ne, “sun karbe iko ne kawai.”
Janar Moyo ya ce “Muna so mu yi bayani dalla-dalla ga daukacin al’umar kasar nan da ma sauran duniya cewa, ba wai sojoji sun karbe mulki ba ne, abinda mu ke yi shi ne muna yayyafa ruwan sanyi ne akan takaddamar siyasa da ta tattalin arziki da ke illa ga kasarmu, wacce idan ba a tashi tsaye ba, za ta iya haifar da mummunar tarzoma a kasar mu.”
Wannan takadda dai ta samo asali ne tun a makon jiya, bayan da Mugabe ya kori mataimakinsa, Emmerson Mnangagwa, tare da zarginsa da cewa ya ci amana da kuma kitsa shirin karbe mulkin kasar.
Da yawa daga dai sun kalli wannan mataki na Mugabe a matsayin wani yunkuri na dora matarsa Grace Mugabe a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, wanda hakan zai ba ta damar maye gurbinsa idan ya yi ritaya ko kuma ya mutu.
A wani taron manema labarai da aka yi ranar Litinin, shugaban dakarun kasar, Janar Constantino Chiwenga, ya yi gargadin cewa zai “shiga tsakani” idan har Mugabe bai daina koran magoya bayan tsohon mataimakinsa ba, wadanda ‘yan jam’iya mai mulki ne ta ZANU-PF
An dai tsare da wasu da yawa daga cikinsu, tun bayan da aka kori mataimakin shugaban kasar a ranar biyar ga watan Nuwamba.
Shugaba Mugabe ya karbi ragamar mulkin kasar ta Zimbabwe ne tun bayan da ta samu ‘yan cin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar alif-dari-tara-da tamanin.
Muna dauke da karin bayani kan wannan dambarwar siyasa bayan kun gama jin labaran duniya.
Ga karin bayani. Da farko za'a ji fashin baki da Farfesa Boube Na Marwa yayi da Hausa kana sai sanarwar sojojin Zimbabwe da Turanci.
Your browser doesn’t support HTML5