Amurka ta yi alkawarin taimakon agajin dala miliyan 20 ga Venezuela, ciki har da abinci da ake bukata sosai da kuma magunguna, amma shugaba Nicolas Maduro ya watsi da taimakon.
WASHINGTON D.C. —
Sojojin Venezuela sun toshe wata muhimmiyar hanya a Ikara kasar don hana shigo da kayan agajin jinkai daga Amurka da kuma wasu kasashen waje.
Jiya Laraba, an ajiye wata babbar motar dako da wasu manyan kwantenonin dakon kaya biyu a tsakiyar wata gada da ta hada Venezuela da Colombia ranar Laraba, da kuma sojoji dauke da makamai dake sintirin a wurin don tisa keyar duk wani yinkurin tsalla iyaka.
Amurka ta yi alkawarin taimakon agajin dala miliyan 20 ga Venezuela, ciki har da abinci da ake bukata sosai da kuma magunguna, amma shugaba Nicolas Maduro ya watsi da taimakon, yana mai cewa Venezuela ba kasar mabarata bace bayan haka wannan zai ba sojojin Amurka damarmamaya.