Harin ya zo ne bayan sa’o’i kadan da ake zargin 'yan tawaye Kurdawa sun ta da bama-bamai da kuma bude wuta a kamfanin sararin samaniya da tsaro na TUSAS.
Washington D.C. —
Sojojin saman Turkiyya sun kai hari kan wuraren mayakan 'yan tawaye na Kurdawa a Iraqi da Syria a matsayin martani ga wani hari da aka kai a wani kamfani mai kula da tsaro na gwamnati.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyar da kuma jikkata fiye da mutum 20.
Ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa an "lalata" wurare fiye da 30 a wannan farmaki na sama, ba tare da yin cikakken bayani game da wuraren da aka kai harin ba.
Harin ya zo ne bayan sa’o’i kadan da ake zargin 'yan tawaye Kurdawa sun ta da bama-bamai da kuma bude wuta a kamfanin sararin samaniya da tsaro na TUSAS.
Ministan cikin gida, Ali Yerlikaya, ya ce maharan biyu — namiji da mace — su ma sun mutu.