Sojojin Syria sun kai hari ta kasa dama ta sama akan garin dake gabashin Ghouta inda ya rage karkashin ‘yan tawaye, kuma sun kashe a kalla mutane 40 inji masu sa ido a wannan yakin.
Gidan talabijin na kasar ya nuno jiya juma’a yadda hayaki ke tashi daga sassa daban-daban na birnin Douma, gari mafi girma a yankin na Ghouta.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sa kai ne suka auka ma garin inda nan ne keda sauran ‘yan tawayen Jaish al-Islam suke rike dashi.
Wannan yakin ya biyo bayan da ‘yan tawayen dake Ghouta ne suka amince da su gitta arewa maso gabashin Aleppo bada matsala ba.
A cikin satin data gabata ne dai Rasha tace kungiyar ta Jaish-al-islam ta amince data bar Ghouta, inda dubun dubatan jamaar kungiyar suke, amma kuma kwaran sai gashi an samu matsala wajen kwashewar nasu, abinda rahotanni suka ce matsalar ta biyo bayan rarrabuwar kawuna ne da aka samu game da kwashewar.
Kungiyar nan mai sa ido dake da babban ofishin ta a Birtaniya da ake kirra Syrian Observatory for Human right tace cikin mutanen da aka kashe su 40 har da kananan yara 8.
Kungiyar tace harinda aka kai ta sama ba mamaki jigir kasar Rasha ce ta kai shi domin ankai ire-iren wadannan hare-haren a sassan birnin daban-daban.