Sojoji Sun Mikawa Gwamnatin Borno Shanun Sata da Suka Kwato

Wasu cikin shanun sata da aka gano a Borno

Jiya rundunar sojojin Najeriya shiya ta bakwai dake birnin Maiduguri ta mikawa gwamnatin jihar Borno wasu shanu kimanin 316 da suka kwato daga masu satar shanu.

'Yan kungiyar Boko Haram ne suke kai hari kan makiyaya kana su kwashe shanusu su sayar su yi anfani da kudin da suka samu domin sayen makamai da ciyar da kansu.

Watan jiya ne rundunar sojojin ta bada sanarwar kame wasu mutane kimanin talatin cikinsu kuwa har da wasu jami'anta guda hudu da 'yansanda biyu da 'yan sa kai ko 'ya kato dagora, da rundunar tace ta samesu da ahannu dumu-dumu a satar shanun.

Kanar Mustapha Anka wanda yayi magana a madadin sojojin shi ya mika shanun ga gwamnatin Borno kamar yadda yace an umurceshi yayi. Wadanda kuma suka kama suna hannun hukuma ana yi masu bincike.

Antoni Janar din jihar Borno shi ya karbi shanun a madadin gwamna da kuma gwamnatin jihar.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Borno Sun Mikawa Gwamnatin Borno Shanun Sata da Suka Kwato - 3' 14"