A kudancin Sudan ta kudu mazauna kauyuka sun ce sojojin kasar da ake kira SPLA sun yi barna a yankin da ake kira Oming, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari wanda ya halaka dakarun kasar takwas, ya jikkata wasu biyar a farkon makon nan.
WASHINGTON D.C. —
Mazauna karamar hukumar Torit ta gabas a yankin na Oming, sun ce mummunar tarozmar ta auku ne ranar Talata.
Sun ce mutane da ake zargin 'yan tawaye ne sun kai hari kan wani ofishin 'Yansanda dake tazarar kilomita 50 da garin Torit suka sace makamai masu yawa.
Daga nan sai gwamnati ta tura sojojin kasar su farauto 'yan tawayen, amma sai aka yi masu kwanton bauna a wuri da ake kira Okuma Mafi domin su bi sawun 'yan tawayen.