A ranar Asabar 18 ga watan Yuli rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da cewa za ta dauki matakin doka akan duk wani dan jarida ko dan gwagwarmaya da ya muzanta rundunar.
Sanarwar ta ce hakurin rundunar ya kai bango akan yadda ake muzanta ta ake kuma zargin ta da abubuwa da yawa don kawai a bata sojin da kuma tsarin tsaron Sudan.
Tun a watan Agustan shekarar 2019 kasar ke karkashin jagorancin gwamnatin hadin gwiwa da galibinta farar hula ne har zuwa tsawon shekaru 3, biyo bayan hambarar da Shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019 bayan da aka kwashe watanni ana zanga-zangar nuna kin jinin mulkin shekara 30 da Shugaban ya kwashe ya na yi.
‘Yan gwagwarmaya sun sha zargin sojojin da gazawa wajan kare masu zanga-zanga a lokacin guguwar zanga-zangar juyin juya halin kasar.