Sojojin Siriya Sun Danna Cikin Manbij Da Ke Aleppo

  • Ibrahim Garba
A wani al'amari mai nuna alamar za a yi ta, sojojin Siriya sun kutsa cikin yankuna masu muhimmancin gaske daura da birnin Manbij mai dinbin muhimmanci. Wannan ko na faruwa ne a daidai lokacin da 'yan tawayen Siriya masu samun goyon bayan Turkiyya ke karce kasa a kusa da Manbij.

Hukumomin Siriya sun bayyana a wata rubutacciyar takarda cewa, sojojin gwamnati sun samu dannawa zuwa cikin wasu muhimman yankuna da ke arewa maso gabashin birnin Manbij da ke karkashin Aleppo.

Sojojin na Siriya sun ce su na masu bayar da tabbacin shirin kare dukkannin 'yan Syria da ma daukacin mazauna cikin birnin.

Kungiyar Dakarun kurdawa Masu Kare Siriya (YPG, a takaice) wadda ita ce babbar kungiyar mayakan Kurdawa a Siriya, ta yi kira ga gwamnatin Bashar al-Assad a yau din nan Jumma'a da ta mayar da Manbij a karkashin kulawarta don ta kare yankin daga barazanar hare-hare daga kasar Turkiyya.

"Mu na masu gayyatar gwamnatin Siriya, wadda mu ma wani bangare ne na ta, da ta tura sojojinta don su kwace wadannan wuraren don su kare Manbij daga duk wata barazana daga Turkiyya," a cewar kungiyar ta YPG a takardar bayanin.