Sojan gwamnatin Syria sun kara dannawa acikin birnin Arewacin kasar na Aleppo jiya Lahadi a kokarin da suke don kwato wannan birni mai muhimmanci dake hannu mayakan yan hamayyar.
Ma’aikatar labarai ta Syria ta rawaito cewa sojojin sun yi alkawarin kyale ‘yantawayen su fice garin lami lafiya muddin zasu bar birnin biyo bayana ruwan bama bamai da aka yi a garin, wanda an fi auna assibitoci a cikinsa.
Ma’aikatan bada agaji sun ce an kai farmaki na biyu a babban asibitin yankin da ta rage a hannun yan tawayena ranar Assabar , a wani kokari da rundunar sojan
gwamnatin Syria da kawayensu na Rasha suke yi na sake kwato birnin baki dayansa.
Babban Jami'in da ke kula da kai kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya fada jiya Lahadi cewar harkokin kiwon lafiya a gabashin Aleppo duk sun tabrbare.
A don haka ya sake yin kira da a tsagaita wuta na dan lokaci don fita da masu neman jinyar gaggawa daga birnin da harkokin kiwon lafiyar ke gab da rushewa.
Rikicin yankin Aleppo da aka kwashe watannin ana yi, ya janyo dimbin kashe-kashen mutane masu tarin yawan gaske, tun lokacinda yakin basasa ya barke a kasar ta Syria sama da shekaru biyar da suka wuce.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya na kiyasin cewa yawan mutanen da aka hallaka a wannan tarzoma ta Syria sun haya mutum dubu 400.