Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Watsi Da Ikirarin Mayakan Boko Haram Na Harbo Wani Jirginsu

Sojojin saman na Najeriya sun ce kwararru na nazarin tantance sahihancin bidiyon da ya nuna harbo wani jirgin saman soja da mayakan Boko Haram suka ce su suka yi.

Rundunar sojojin Najeriya ta yi watsi da ikirarin da mayakan Boko Haram suka yi na cewa su suka harbo jirgin saman sojan da ya bace bayan da aka daina samun bayanan sadarwarsa daga na’urar da ke bibiyar jirage a ranar Laraba.

Ranar Juma’a mayakan Boko Haram suka fidda wani bidiyo da ya nuna wani jirgi ya kama da wuta da kuma tarkacen jirgin da ya fado, har ma da gawar wani soja. Bisa ikirarinsu, su suka harbo jirgin a yankin jihar Borno.

A wata sanarwa ta shafin Facebook, rundunar sojojin saman ta ce ko da ya ke ana kan nazari sosai akan bidiyon, amma ga dukkan alamu an yanke wasu abubuwa a bidiyon ta yadda ya nuna kamar an harbo jirgin ne.

Karin bayani akan: Boko Haram, Jirgin Yakin Saman, jihar Borno​, Sojojin Najeriya, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce a bayyane ya ke mayakan na amfani da farfaganda ne wajen daukar alhakin abinda ba su suka yi ba, kuma ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi wannan bidiyon da ke yawo har sai an kammala bincike kan yadda jirgin ya fado.

A wata sanarwa ta Twitter a baya, rundunar sojojin ta fadi cewa matukan jirgin mai lamba NAF 475, sun hada da Flight Lieutenant John Abolarinwa da Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele.