Sojojin Rwanda Sun Yi Amfani Da Albarusai Wajen Tarwatsa 'Yan Gudun Hijira

Sojojin kasar Rwanda sunyi anfani da albarussai na gaske wajen tarwatsa gungun wasu ‘yan gudun hijira na kasar Congo-Kinshasa da suka yi kokarin gudu don ficewa daga sansanin da aka ajiye su, wanda suke korafi game da halin da yake cikin.

‘Yan gudun hijira tsakanin dubu uku zuwa dubu hudu ne suka yi tattakin kamar mil biyu daga sansanin nasu na Kiziba zuwa ofishin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya dake ke a gundumar Karongi a yammacin Rwanda din don bayyana korafe-korafen nasu.

‘Yan gudun hijiran na neman a chanja musu kasar zama ne, wanda suka ce idan ba’ayi musu hakan ba, zasu taka kafa su koma kasashensu na asali.

Yazuwa yanzu dai da gwamnatin Rwanda da Majalisar Dinkin Duniya, ba wacce tayi magana da ‘yan gudun hijiran.