Nigeria tace sojojinta sun kaddamar da hare haren maida martani akan yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram wadanda a halin yanzu suke mamaye da garin Baga da kuma wani muhimmin sansanin soja a arewa maso gabashin kasar.
A ranar Asabar data shige yan kungiyar Boko Haram suka mamaye garin Baga. Gwamnatin Nigeria tace tun lokacin ne dake bin diddigin yan yakin sa kan, kuma ta kaddamar da hare hare da jiragen saman yaki akan yan tawayen.
A ranar uku ga wannan wata na Janairu 'yan Boko Haram suka fatattaki sojojin Nigeria daga garin bayan anyi mumunar bata kashi.
Jami'ai sunce tun lokacin, yan Boko Haram sun kona illaharin gari na Baga da kauyukan da suke kusa. Al'amarin daya tilastawa dubban mutane arcewa zuwa tsibirai a tapkin Chadi ko kuma Maiduguri baban birnin jihar Borno.
An kiyasta cewa farar hular da aka kashe cikin makon jiya sun kai dubu biyu.
Wannan tarzoma ta barke ne a yayinda yan takara suka fara yakin neman zaben shugaban kasa dana gwamnoni da kuma wakilan Majalisun Nigeria da za'a yi a watan Fabrairu idan Allah ya kaimu.
Da kakausan lafazi ake ta cacakar shugaba Goodluck Jonathan wanda yake son a sake zabensa a saboda ya kasa murkushe yan Boko Haram wadanda aka dorawa laifin kashe dubban mutane cikin shekaru biyar da suka shige.