Rundunar sojin Najeriya ta ce zata rika sa idanu sosai a makarantun sakandare na mata dake yankin arewa maso gabashin kasar domin tabbatar da tsaro a kansu.
Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sanin makomar yaran makarantar sakandare ta mata dake Dapchi cikin jihar Yobe da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace cikin makon jiya.
Yayinda yake bude wani sabon ofishin sojojin da wajen ba da horo a barikin sojojin dake Kwantagora daraktan ayyuka da ba da horo na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar David D Ahmadu ya ce kodayake aikin tsaro a makarantun na 'yan sanda ne da sauran jami'an tsaro amma hakan ba zai hanasu sanya idanu a makarantun ba.
Manjo Janar David D Ahmadu wanda ya wakilci hafsan hafsoshin sojojin Janar Tukur Yusuf Buratai ya bukaci hadin kan 'yan jarida da jama'ar gari musamman a yakin da suke yi da 'yan ta'adda.
Acewar Janar Ahmadu 'yan jarida ya kamata suna fadin gaskiyar abun da ya faru. Ya kira 'yan jarida su dinga ba da labarin da zai kai ga cafke masu tada zaune tsaye a kasar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5