Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojoji sun kwato wasu mutane 19, ciki har da wasu 'yan kasashen waje, da ake yin garkuwa da su a yankin kudancin kasar mai arzikin man fetur.
Rahotannin kafofin labarai dake fitowa daga Najeriya sun ce mutanen da aka kwato sun hada da Amurkawa biyu, da Faransawa biyu, da dan kasar Canada daya da kuma wasu mutanen biyu 'yan kasar Indonesiya, dukkansu wadanda aka sace a makon da ya shige daga wani dandalin hakar mai cikin teku na kamfanin Britaniya mai suna Afren.
Suka ce wannan farmakin da sojoji suka kai ya kuma kwato wasu ma'aikata da aka sace daga wani dandalin hakar mai na kamfanin Exxon Mobil dake Jihar Akwa-Ibom a wannan makon.
Ma'aikatar harkokin wajen faransa ta tabbatar larabar nan cewa an kwato 'yan kasarta su biyu.
Yankin Niger-Delta mai arzikin mai a kudancin Najeriya yana dauke da kungiyoyin 'yan daba dake satar man fetur da kuma sace mutane su na yin garkuwa da su domin a biya su kudaden fansa. Haka kuma, akwai kungiyoyin tsagera dake ikirarin cewa su na gwagwarmayar ganin an saka wa mutanen yankin saboda arzikin man da ake tona daga yankinsu.
Babbar kungiyar tsagera ta yankin Niger-Delta, MEND, ita ce ta dauki alhakin sace wadannan mutane da aka yi garkuwa da su a cikin wannan watan.