Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram 19 A Damboa

Sojojin Najeriya

Shalkwatar rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da aukuwar wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Damboa. Rundunar ta kuma ce sojojinta sun kashe ‘yan ta'adda 19.

Wannan harin dai ya faru ne a wani babban sansanin sojoji da ake kira Super Camp 2 dake garin Damboa a jihar Borno, inda suka yi wa sansanin tsinke ta bangarori hudu.

A lokacin da mayakan suka dumfari sansanin cikin wasu motoci dake dauke da manyan bindigogi suna ta harbe-harbe, jajirtattun sojojin sun nuna masu cewa ruwa ba sa'ar kwando ba ne har sai da suka kashe kimanin mayaka goma sha tara, suka kuma kwato wasu motocin yaki da kuma manyan bindigogi kirar AK 47, da bindigogi masu sarrafa kansu da rokoki.

Kanar Aminu Ilyasu, ya ce wannan fafatawar na daya daga cikin babbar nasarar da aka cimma a fafatawar da aka yi tun kamawar wannan shekara. Ko da yake, sojoji uku sun rasa rayukansu, wasu hudu kuma sun sami rauni wadanda a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin sojin.

Masanin tsaro Manjo Bashir Galma mai ritaya, ya ce wannan hobbasan na dakarun ya biyo bayan irin horon da suka samu ne wanda kuma ya cancanci ‘yan kasa su yaba don kara masu kwarin gwiwa.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram 19 A Damboa - 3'24"