Mukaddashin Darektan yada labarai na runduar sojojin kasa na Najeriya, kanal Sani Kukasheka usman, wanda ya bayyana haka a hira da yayi da Ibrahim Alfa Ahmed, yace bayanan sirri da suka samu ta hanyoyi daban daban ne suka taimaka wajen gano mabuyar 'yan Boko Haram.
Kanal Sani Usman yace, sojojin da suka kai harin wadanda suke karkashin bataliya ta 21 na birgade 26 dake Gwoza, sune suka jagoranci farmakin da suka kai a wurare da ake kira Dure ta daya, data biyu, da Jango, da kuma Dibiye a Sambisa.
Kakakin rundunar mayakan kasar, yace yanzu 'yan ta'addan sun fito da wani salo na dana tarko da kananan rediyo na hanu, lamari da ya jikkata sojojin Najeriya su uku. Duk da haka yace suna murmurewa.
Nasarar da suka samu ne ma tasa kwamandan shiyya ta bakwai mai helkwata a Maiduguri,Birgediya Janar Victor Okwudi Ezugwu,ya ziyarci dakarun inda ya jinjina msusu. Yace sojojin Najeriya ba zasu yi ksa a guiwa ba ha r sai sunga bayan 'yan ta'adda.
Wannan mataki na kakkabe 'yan binidgar yana ci gaba sosai. Domin ko akwanin baya, wata runduna ta 331 data 231sun kai farmaki kan mabuyar 'yan binidgar a yankin karamar hukumar Biu, suka kashe 'yan ta'addan da dama, kuma suka gano makamai.
Kukasheka yace, saboda haka yanzu kudancin Barno ya sami sauki daga hare-haren da 'yan binidgar da suke Dosa-ko indoksa suke yawqan aki musu.
Ga karin bayani.