Muna Kara Samun Galaba A Kan 'Yan Ta'adda A Arewa - Rundunar Sojin Najeriya

  • VOA Hausa

Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai

Shelkwatan tsaron Najeriya ta ce an kashe wani kasurgumin dan ta’addan nan Mai Hijabi a wani aiki da dakarunta suka gudanar a jihar Jigawa a wannan mako.

Shelkwatan ta ce wannan wani bangare ne a kokarin da ta ke yi domin tarwatsa karfin kungiyoyin ‘yan ta’addan a duk fadin arewacin kasar.

Darektan kula da ayyukan kafafen labarai a ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi wa ‘yan jarida a kan ayyukan dakarun sojan a wannan mako.

Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

Ya ce an kashe ‘yan ta’adda 165 kana aka kama wasu 238 da ake zarginsu da aikata .

Buba ya kara da cewa, “aikin da muka gudanar ya raunata karfin yaki da kungiyoyin ‘yan ta’addan suke da shi da shugabanninsu. Alal misali, akwai wani kasurgumin kwamandan ‘yan ta’adda da ake kiransa Mai Hijabi da aka kashe shi a jihar Jigawa a cikin wani gumurzu a wannan mako. Don haka sojoji suna kara samun ci gaba a duk fagagen daga da suka gudanar da ayyukansu.

“A yayin sake duban ayyukan mako, sojojin sun kashe mutum 165, sun kuma kama wasu 238 kana suka kubutar da mutane 188 da aka yi garkuwa da su.”

Buba ya ce sojojin sun kuma cafke wasu mutane 35 da ake zargi barayin man fetur a yankin kudu maso kudancin kasar, wanda kuma suka musanta satar mai da kudinsa ya kai Naira miliyan 688 da dubu 125 da 150.

“Sojoji a yankin Niger Delta sun gano wasu ramuka biyu, da kwale-kwale 58 da kuma tankokin adana mai 39 kuma tuni suka lalata su. Sauran kayan da aka kama sun hada da murhun dafuwa, kalanguna 35, da babur guda, da mai tayoyi uku, da jirgin ruwa mai tsananin gudu da motoci 13 da wuraren tace mai 65 ta barauniyar hanya. Sojojin sun kwato lita 789,200 na danyen mai da aka sace da kuma lita 64,950 na AGO da aka tace ba bisa ka'ida ba," in ji shi.

Buba ya ce sojojin sun kwato makamai iri-iri 153 da kuma albarusai iri-iri 2,182.