Rundunar sojan Najeriya ta fitar da sanarwa dake cewa, wasu ‘yan Boko Haram 76 sun gamu ajalinsu a lokacin da suke kokarin kai hari akan sansanonin jami’an soja a kauyen Maitale dake garin Kangarwa a arewacin Borno.
Sanarwa ta kara da cewa, sojojin Chadi sun hallaka wasu ‘yan Boko Haram 48, bayan da suka yi kokarin kai wa sansanin sojojinsu hari.
Haka kuma rundunar ta kuma tarwatsa wasu ‘yan Boko Haram su 76, sai dai abin takaici shine rundunar ta rasa wasu jami’anta 7, wasu 17 kuma suka ji rauni. Tuni dai babban hafsan sojan Najeriya Janar Tukur Buratai ya jajantawa iyalan mamatan, ya kuma yi alkawarin basu kulawa da samar da magani ga wadanda suka jikkata.
A daya bangaren kuma, sojojin Chadi guda takwas sun rasa rayukansu, haka kuma an kashe wasu mayakan Boko Haram 48 sakamakon arangamar.
Hare-hare daga mayakan Boko Haram ke kaiwa na ci gaba da daukar hankalin al’ummar dake yankin tafkin Chadi.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5