Game da ‘yan bindigar da suka mamaye Otal din nan Radisson Blu da ke Bamaco a kasar Mali, rahotannin na nuna cewa a yanzu haka sojojin Mali da tallafin na Majalisar Dinkin Duniya da wasu jami’an tsaron musamman sun sami kawo karshen garkuwar da aka yi da jama’a a ciki.
An ga jama’a na ta murna suna Shewa tare da jinjinawa sojoji suna kiran “Sai Sojojin Mali”. Wani mazaunin Mali mai suna Alou Diallo ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, an fafata sosai da ‘yan bindigar inda daga baya aka karkashe su a aka ceci jama’ar da suka yi garkuwar da su.
Ya fadawa abokin aikinmu Ibrahim Garba yadda maharani suka isa Otal din a motocin a irin motocin nan na ma’aikatan ofishin jakadanci. Inda daga baya suka bude wuta suka kame jama’a. Sannan sojojin Malin sun ta korasu har sai da suka kaisu kuryar Otal din can hawa na bakwai sannan suka murkushe su.
Your browser doesn’t support HTML5