Shekaru uku bayan kungiyar kwancen tsaro ta NATO ta kawo karshen aikin fafatawa da take yi a kasar Afghanistan, sojojin kundubalan Amirka sun koma lardin Helmand.
Sojojin kundubalan Amirka dana kungiyar NATO sun halarci wani biki da aka yi jiya Asabar na mika musu kulawa da lardin Helmand
To amma maimakon fafatawa a wannan karo zasu bada horo da shawara ga mayakan Afghanistan, wadanda suke yarbe gumi wajen kokarin fatattakar yan tawayen kungiyar Taliban
Sojojin sun koma kwana daya bayan kungiyar Taliban ta bada sanarwar kaddamar da fafatawa, lokacin da take zafafa kai hare hare.
Farkon wannan wata sojojin Afghanstan suka yi hasarar sosai lokacin da 'yan kunar bakin wake na Taliban da suka yi shigar burtu kamar sojojin Afghanistan suka kashe sojoji dari da talatin da biyar.